Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta saki babban Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris, da aka dakatar daga hannun ta.
Hukumar ta samu umarnin kotu na tsare Akanta Janar na Tarayya Ahmed Idris na tsawon kwanaki.
Hukumar ta kama Ahmed Idris ne bisa zargin almundahanar Naira biliyan 80. A ranar Alhamis din nan ne dai hukumar EFCC ta sake shi.