Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), ta kara tsawaita yajin aikin da take yi har zuwa makonni 12.
An dauki matakin ne a wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kasa (NEC) da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.
Taron gaggawa, wanda ya samu halartar manyan hafsoshi da shugabannin reshe, an fara shi ne a ranar Lahadi, kuma ya ƙare da sanyin safiyar Litinin.