Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun yi garkuwa da wasu fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba daga tashar jirgin kasa da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, ya ce, mutane da dama sun jikkata a yayin harin.
DAILY POST ta tattaro cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su na dakon shiga jirgin kasa zuwa garin Warri da ke jihar Delta a lokacin da maharan suka mamaye tashar suna harbe-harbe.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, har yanzu ba a san ko wani ya mutu a lamarin ba.