Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da yin garkuwa da Okechukwu Okoye, dan majalisa mai wakiltar mazabar Aguata 1 a majalisar dokokin jihar Anambra.
An yi garkuwa da Mista Okoye, dan asalin Isuofia, al’umma daya da Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra, a Aguata ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Toochukwu Ikenga, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN lamarin a ranar Lahadi.
‘Yan sandan sun ce, an samu nasarar gano bakar Siena SUV na dan majalisar, wadda yake tukawa kafin faruwar lamarin.
Mista Ikenga, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce ‘yan sanda sun kaddamar da farautar masu garkuwa da mutane domin kubutar da dan majalisar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma tabbatar da kisan wani dan kungiyar ’yan banga, wanda ke kan babur a garin Oko da ke Anambra a ranar Lahadi.
Mista Ikenga ya kuma ce, marigayin yana sanye ne da kayan tsaro na musamman, amma ba dan sanda ba ne.