fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: An kama matashin da ya aiko da bindigogi 8 daga Abuja zuwa Kano

Date:

Kungiyar ‘yan sintiri a tashar motar Zuba da ke Abuja, ta kama wani mutum da bindigogi takwas da ya yi niyyar kai su Jihar Kano.

Jaridar DailyTrust ta ambato shugaban ‘yan sintirin da ke yankin, Yahaya Madaki, yana cewa lamarin ya auku a ranar Laraba.

Ya ce, mutumin ya je tashar motar ne da misalin karfe biyu na rana inda yake neman motar da za ta je Kano don bayar da sakon.

Daga nan ne sai ya samu direban da ke lodi zuwa Kano ya mika masa sakon da aka sanya a kwali da kuma lambar wayar mutumin da zai kai wa sakon a Kano.

A cewar jaridar, an caji mutumin Naira dubu 10 kudin dakon kayan, kuma nan take ya ciro ya bayar, daga nan ne sai direban motar ya nemi ya ji ko mene ne a cikin kwalin daga nan ne sai mutumin ya nemi ya tsere to amma an kama shi.

Yahaya Madaki ya ce, ko da aka bude kwalin an ga bindiga samfurin AK-47 biyar, sai kananan bindigogi uku.

Yanzu haka mutumin na wajen ‘yan sanda inda suke gudanar da bincike a kan lamarin.

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp