Rundunar ‘yan sanda a garin Tuckahoe da ke birnin New York na kasar Amurka, ta gano gawar wani tsohon jami’in diflomasiyyar Najeriya, Ambasada Ejeviome Otobo, wanda aka gani na karshe a unguwarsa a ranar 15 ga watan Yunin 2022.
Rundunar ‘yan sandan Tuckahoe a ranar 19 ga watan Yuni ta sanar a wani sako da ta wallafa a shafin Facebook cewa, Etobo ya bace kuma ya nemi bayanai daga jama’a.
Jami’in diflomasiyyar mai shekaru 70 a lokacin mutuwarsa, ya taba rike mukamin Darakta kuma mataimakin shugaban ofishin tallafawa samar da zaman lafiya a shelkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York tsakanin Disamba 2006 da Oktoba 2013.
A ranar 24 ga watan Yuni, ‘yan sanda sun sanar da cewa, an gano Etobo gawarsa tare da aika sakon ta’aziyya ga iyalansa.