An ga jinjirin watan Ramadan a wurare daban-daban a kasar Saudiyya, wanda ke nufin za a fara azumin watan Ramadan a kasa mai tsarki a ranar Asabar.
Har yanzu dai ba a fitar da sanarwar ganin watan Ramadana a Najeriya ba, amma a ranar Alhamis mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya bukaci al’ummar Musulmi da su lura da ganin watan.