Mutane da dama ne suka jikkata, sakamakon rikicin da ya barke a karamar hukumar Aninri da Nssuka na jihar Enugu yayin taron jam’iyyar PDP.
An tattaro cewa ‘yan barandan da suka jefa kujeru da kwalabe a Nsukka a ranar Asabar din da ta gabata sun yi amfani da makamai cikin ‘yanci a daidai lokacin da mata da wasu suka tsallake rijiya da baya a kokarin tserewa.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai cewa, batun wanda ke wakiltar al’ummar Nsukka/Igbo-Eze ta Kudu a Majalisar Wakilai, an ce shi ne ya haddasa rikicin a yayin taron.
Haka kuma a wani taron siyasa da aka gudanar a Ndeaboh a karamar hukumar Aniiri, da dama sun samu munanan raunuka yayin da wasu ke kwance a asibiti sakamakon wani mummunan hari da aka kai a yayin taron siyasa na PDP.
A martanin da ya mayar, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan rikicin da ya rikide wa taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a karamar hukumar Aninri ta jihar Enugu a karshen mako da kuma mummunan harin da aka kai wa magoya bayansa da abokan siyasarsa a yayin taron da aka ce a Ndeaboh.
Ekweremadu ya tuna cewa, harin ya bar mutane da dama ciki har da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Aninri a majalisar dokokin jihar Enugu, Hon. Chinedu Okwu wanda ya samu munanan raunuka, kuma yana kwance a asibiti ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata laifin.