Gabanin zaben fidda gwani na gwamna da za a yi a ranar Laraba a jihar Enugu, wasu jiga-jigan ‘yan takarar gwamna uku na jam’iyyar PDP sun janye daga takarar.
‘Yan takarar uku sun bayyana ficewarsu ne a wata takarda da suka fitar daban-daban, kuma suka mikawa shugabannin jam’iyyar sa’o’i kadan kafin zaben fidda gwani na gwamna.
Wasikar janyewa Ekweremadu ta samu sa hannun Hon. Charles Asogwa, Darakta-Janar, Kungiyar Kamfen na Ikeoha.
Ya ce, “Muna so mu sanar da magoya bayanmu da ‘yan Nijeriya cewa, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma jigo a jam’iyyar da ke neman takarar gwamna a jihar Enugu, Sanata Ike Ekweremadu, ba zai halarci zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP da za a yi a ranar Laraba 25 ga watan Mayu ba. 2022.”