fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan ta’adda sun harbe matafiya 5 har lahira a Katsina

Date:

An bayar da rahoton mutuwar fasinjoji biyar tare da raunata wasu uku bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan wata mota a kan hanyar Yan Tumaki zuwa Danmusa a jihar Katsina, da safiyar Asabar.

Karamar hukumar Danmusa dai na daya daga cikin yankunan da ake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina, inda ta raba iyaka da dajin Rugu da ake fargabar da kuma yankunan Safana, Kankara da sauran al’ummomi a jihar Zamfara inda ‘yan fashi ke yawan kai farmaki.

Wani ganau wanda ya bayyana sunansa da Musa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, yawancin fasinjojin sun fito ne daga Benin a Jihar Edo yayin da daya ke dawowa daga Babban Birnin Tarayya (Abuja) inda ya je kawo kaji.

Ya ce, fasinjojin ‘yan asalin garin Gobirawa ne da Kaigar Malamai a jihar Katsina.

“Motar mai kirar Golf ce, ta taso daga Yantumaki zuwa garin Danmusa da safe. Fasinjojin sun kwana a Yantumaki, saboda sun isa can da daddare. Da safe suka hau motar zuwa garin Danmusa inda zasu dauki babura zuwa garuruwansu.

“Amma an kai wa motar harin ‘yan mintoci kadan da barin Yantumaki. Abin da ya faru shi ne ‘yan fashin sun hango motar inda suka yi kokarin tsayar da motar amma direban ya ki tsayawa, lamarin da ya sa ‘yan bindigan suka fara harbin su. Motar ta yi damina ta bugi bishiya,” inji shi.

Musa ya ce, barayin sun gudu ne a lokacin da hatsarin ya afku.

“An kuma sanar da ‘yan sanda a Danmusa, inda suka dauko gawarwakin, kuma suka kai wadanda suka jikkata uku asibiti. Mun yi jana’izar wadanda suka mutu, yayin da sauran mutane uku ke karbar kulawar lafiya,”

Musa ya kara da cewa. Dalilin harin
Wata majiya da ke zaune a yankin amma ba ta so a bayyana sunanta, ta ce, ‘yan bindigar na kara kai hare-hare mai yiwuwa, domin daukar fansa kan jami’an tsaro da suka far musu.

Hatta kisan da aka yi wa fasinjojin an ce ‘yan fashin sun fusata ne, saboda ‘yan sanda da sojoji sun hana su satar shanu masu tarin yawa a ranar Alhamis din da ta gabata.

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp