Ƴan bindiga sun sace, iyalan wani ɗan Majalisar Dodokokin Jihar Zamfara a garin Jangebe da ke jihar.
‘Yan bindgar da ake zaton masu garkuwa da mutane ne domin karɓar kuɗin fansa sun dirar wa gidan Honorabul Aminu Yusuf Ardo ne jiya Alhamis da dare, inda suka sace matarsa da duka ya’yansu hudu ƙanana.
Sun kuma sace wasu maƙwabtan dan siyasar, kamar yadda wani mazaunin unguwar da gidan ɗan majalisar yake ya shaida wa BBC.
Danna hoton da ke ƙasa ku saurari rahoton Isha Khalid daga Abuja