Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP, Ademola Adeleke, ya kada kuri’arsa a zaben gwamnan jihar Osun da ke gudana.
Adeleke ya kada kuri’a a Unit 009, Ward 02, Abogunde/Sagba, Ede North a jihar Osun.
A cewar hukumar zabe mai zaman kanta, Ede ta Arewa tana da masu kada kuri’a 71,750 domin zaben gwamna, da rumfunan zabe 151 da kuma wuraren rajista 11 .
Har ila yau, Ede ta Kudu na da masu kada kuri’a 54, 880, da rumfunan zabe 89 da kuma wuraren rajista 10 inda ake sa ran masu kada kuri’a za su kada kuri’a.