Bayanai daga birnin Maiduguri na jihar Borno na cewa an samu ɓullar cutar ƙyandar biri a ɗaya daga cikin sansanonin da aka tsugunar da mutanen da ambaliya ruwa ta raba da muhallansu.
Cikin wata sanarwa da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA, ta fitar ta ce tawagar jami’an lafiyarta tare da tallafin ma’aikatan Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO da na hukumar raya ƙasashe ta Amurka da, USAID sun samu nasarar keɓe wadda ake zargi ta kamu da cutar tare da mahaifiyarta da kuma mutanen da ake kyautata zaton sun yi mu’alama da marar lafiyar.
Mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa ‘yar tata ta fara fitar da ƙuraje a jikinta tsawon mako biyu da suka gabata, sai dai babu wani daga cikin ‘yan uwanta da ya nuna alamun cutar.
Tuni hukumomin lafiyar jihar suka ɗauki samfurin jininta domin faɗaɗa bincike, yayin da take ci gaba da samun kulawar likitoci.
Hukumar ta NEMA ta kuma ce tuni suka sanar da hukumomin da lamarin ya shafa, ciki har da hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta NCDC.
Haka kuma hukumar ta NEMA, ta umarci mutane da ɗauki matakan kariya domin daƙile yaɗuwar cutar a cikin sansanin, ciki har da yawaita wanke hannu da tsaftace muhallin.