Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da bullar cutar kyandar biri a kasar, inda ta kasance kasa ta farko da ta sanar da hakan a yankin Gabas ta Tsakiya.
A ranar Talata Jamhuriyar Czech da Slovenia sun sanar da bullar cutar, hakan ya kai adadin kasashe 18 da cutar kyandar biri ta bulla baya ga tushenta wato Afirka.
Ana sa ran adadin wadanda suka kamu da kasashe su karu.
Kyandar biri ta barke a kasashen turai, da Australia da Kuma Amurka. Ma’aikatar lafiya a Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce wanda ya kamu da cutar ya dawo daga balaguron da ya yi a yammacin Afirka, kuma tuni ana ba shi kulawar da ta dace a asibiti.
Alamomin cutar kyandar biri sun hada da zazzabi mai zafin gaske da kasala da kuma fesowar kuraje.
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce za a iya shawo kan yaduwar cutar matukar an bi dokoki da shawarwarin hukumomin lafiya. In ji BBC.