Hukumomin lafiya a Indiya sun ƙaddamar da bincike bayan mazauna ƙauyuka a jihar Maharashtra sun shiga wani yanayi na zubewar gashin kansu haka kawai.
Waɗanda lamarin ya shafa sun ce sun ji ƙaiƙayi mai tsanani a jikinsu cikin kwana uku zuwa huɗu yayin da gashin nasu ke zubewa.
Cutar ta firgita mazauna yankunan, inda wasu ke yi mata laƙabi da “cutar sanƙo”.
Likitoci na zargin gurɓacewar ruwa za ta iya zama dalili kuma tuni suka fara ɗaukar samfur daga yankin domin gudanar da gwaji, ciki har da na gashi da fatar mutanen.