Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya, NCDC ta ce kimanin 1,191 ne suka rasu sakamakon kamuwa da cutar mashaƙo daga watan Mayun 2022 zuwa yanzu a sassan ƙasar.
Hukumar ta kuma cewa mutum 28,000 ne suka kamu da cutar.
Dokta Muzammil Sani Gadanya, babban jami’in kula da ayyukan daƙile cutar mashakon ne a hukumar ta NCDC, ya ce ana bin matakan da suka dace domin gano waɗanda suka kamu da ita, don kuma yi masu magani.