fidelitybank

Cutar Mashako ta yi ajalin Yara hudu a Kano

Date:

Rahotanni na cewa cutar mashaƙo wadda aka fi sani da Diphtheria a turance, ta yi sanadiyar mutuwar yara huɗu yan gida ɗaya a unguwar Hotoron Yan Dodo, dake ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano.

Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru a cikin makonni biyu.

Mahaifin yaran, Malam Yusuf Maitama, ya bayyana cewa ƙaddarar ta fara ne da ƙaramin ɗansa mai ƙasa da shekaru biyar, wanda ya fara fama da zazzaɓi da ciwon maƙogwaro kafin daga bisani ya rasu. Bayan haka kuwa, sauran uku daga cikin ‘ya’yansa suka nuna irin waɗannan alamomin, duk da ƙoƙarin ceto su, amma sun rasu, sai babbar ‘yarsa ce kaɗai ta tsira bayan an kai ta asibiti cikin gaggawa. Kamar yadda jaridar Daily News 24 Hausa ta rawaito.

Rahotanni sun nuna cewa yaran sun nuna alamomin cutar ta mashaƙo irin su zazzaɓi mai zafi da ciwon maƙogwaro.

Bayan faruwar lamarin, jami’an lafiya sun kai ziyara gidan, inda suka tsaftace muhallin tare da yi wa sauran yara rigakafin cutar a unguwar, domin hana yaduwar ta.

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware asibiti na musamman domin kula da masu fama da cutar, tare da tabbatar da cewa ana bayar da rigakafi da magani kyauta ga dukkan yara. Haka kuma ta yi kira ga iyaye da su tabbatar da yin rigakafin yara da kuma gaggauta kai su asibiti idan aka fara samun alamomin cutar.

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kwallaye 6 da aka zurawa Santos a raga ta sanya Neymar ya fashe da kuka

Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin...

Hukumar Shari’a ta magantu kan sadakin dubu 20 da ya yamutsa hazo a Kano

Hukumar shari’a ta jihar Kano, ta ce ba a...

Cutar Mashako ta yi ajalin Yara hudu a Kano

Rahotanni na cewa cutar mashaƙo wadda aka fi sani...

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...
X whatsapp