Gwamnatin jihar Ondo a ranar Lahadin ta ce, adadin mutane 34 ne suka mutu, sakamakon cutar zazzabin Lassa a jihar daga watan Janairu zuwa yau.
Farfesa Francis Faduyile, mashawarci na musamman ga gwamnan jihar kan harkokin kiwon lafiya ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Akure ranar Lahadi.
Faduyile ya ce, jihar ta samu mutane 227 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kananan hukumomi shida a cikin wannan lokacin.
A cewarsa, kananan hukumomin su ne Owo, Ose, Akure ta Kudu, Akoko Kudu-maso-Yamma, Akure ta Arewa da kuma Ondo ta Yamma.
Faduyile ya kuma ce an tabbatar da bullar cutar guda uku a tsakanin ma’aikatan lafiya a jihar.