Cibiyar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta ƙasa NCDC ta ce, a cikin ƙasa da wata uku an samu mutane 784 da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar zazzaɓin Lassa inda mutum 142 suka mutu a faɗin jihohin 23.
A wani saƙo da cibiyar NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an samu waɗanda suka kamu da cutar ne daga 1 ga watan Janairu zuwa yanzu.
NCDC ta ce an samu yawaitar ɓullar cutar ne a jihohin Edo da Ondo da Ebonyi da Bauchi da Taraba da Benue da Rivers da Plateau da Nasarawa.
Haka kuma cibiyar ta ce an samu aƙalla mutum ɗaya da ke ɗauke da cutar a cikin jihohin ƙasar 23.
NCDC ta ce kashi 71 na sabbin mutanen da suka kamu da cutar an same su ne a jihohin Ondo da Edo da Bauchi, yayin da aka samu kashin 29 a sauran jihohin ƙasar shida.
Cutar Lassa wata ƙwayar cuta ce ta ‘Virus’, mai haddasa tsananin zazzaɓi da ɓullar jini a jikin wanda ya kamu ta ita, wanda ake kira a Turance – ‘viral heamorraghic fever’.
A wasu lokuta cutar kan zo da wasu alamomi kamar mura da mashako da samun matsalar numfashi.
Asalin cutar ana samunta ne daga wasu nau’in ɓeraye da ake kira ‘multimammet rats’ a Turance.