Gwamnatin jihar Oyo ta hannun ma’aikatar lafiya a ranar Alhamis ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa a jihar, tare da mutuwar likitoci biyu da wani ma’aikacin asibiti.
Da yake karin haske ga manema labarai a ofishinsa da ke sakatariyar jihar, Agodi Ibadan, kwamishinan lafiya na jihar, Ode Ladipo, ya tunatar da yadda gwamnatin jihar ta kara himma wajen dakile bazuwar cutar mai saurin kisa, tun lokacin da aka fara samun bullar cutar a jihar tun a watan Janairu, 2022.
Ya ci gaba da cewa, an kwantar da likitocin da adadinsu ya kai kusan hudu a wata cibiyar lafiya mai zaman kanta a farkon makon nan, amma mutuwar uku ta faru bayan haka.