Batun nan na yi wa kasafin kudin 2023 na gwamnatin tarayya ciko da majalisar dattawa ke tuhumar ma’aikatar kudi ta kasar na ci gaba tayar da kura.
Kan wannan batun, Ministar jin kai ta aika wa takwararta ta ma’aikatar kudi wata wasika wadda a ciki ta dora alhakin bayyanar wasu naira biliyan 206 cikin kasafin kudin ma’aikatarta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin wadannan ma’aikatun gwamnatin biyu.
A makon jiya, yayin da ministar jin kai ta gwamnatin Najeriya ta halarci zaman majalisar dattawan kasar domin kare kasafin kudin ma’aikatarta, wani batu ya taso da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Wani mamba na kwamitin ayyuka na musamman na majalaisar dattawan, Sanata Elisha Abbo, ya tambayi Minista Sadiya Farouk yadda – kamar yadda ya ce – yadda wasu bakin naira biliyan 206 suka bayyana cikin kasafin kudin ma’aikatar jin kai, wadda ke ƙarƙashin kulawarta.
Rahotanni a jaridun Najeriya sun ruwaito Minista Sadiya Farouk na dora alhakin bayyanar wadannan biliyoyin nairorin kan ma’aikatar kudi ta kasar.
Lamarin ya kai ga Minista Sadiya Farouk ta rubuta wata wasika kai tsaye ga takwararta, wato ministar kudi Zainab Ahmed, kuma a ciki ta nanata cewa ba ta hannu a wannan kutsen da kudaden suka yi wa kasafin kudin ma’aikatar tata, kuma ta dora laifin haka kan ministar.
To ma’aikatar kudi ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta kare minista Zainab Ahmed daga tuhumar da minista Sadiya Farouk ta yi kan batun.
To idan akwai wani darasi da za a iya cewa na koya, shi ne har yanzu Najeriya ba ta iya kawar da batun nan na yi wa kasafin kudin kasar cuse ba, ta hanyar saka wasu kudade da tun farko ba a amince da su ba a hukumance.
Wani abin da ‘yan Najeriya kuma za su so gani shi ne ko wannan bayanin da ma’aikatar kudin Najeriya ta fitar zai gamsar da majalisar dattawar kasar, da kuma matakin da zai biyo baya.