Ƙungiyar Atletico Madrid ta ɗauko ɗan wasan tsakiyar Ingila, Conor Gallagher daga Chelsea a kan farashin da ake hasashen zai kai £33m.
Ɗan wasan mai shekara 24 ya sanya hannu a kwantiragin shekara biyar da ƙungiyar ta Laliga.
Gallagher ya kasance a Chelsea ne tun yana ɗan shekara shida, sannan ya cigaba da samun horo har ya kai ga fara buga wasa, inda ya buga wasa 90, sannan ya zura ƙwallo 10.
Kakar bana ce dai shekararsa ta ƙarshe a Chelsea, inda ƙungiyar ta sayar da shi domin gudun rasa shi a kyauta a kakar baɗi.
Shi kuma ɗan wasan gaban Atletico Joao Felix, shi ma mai shekara 24, zai koma Chelsea.
Ya buga wa Ingila wasa 18 tun bayan da ya fara shiga ƴan wasan tawagar a 2021, kuma yana cikin ƴan wasan tawagar da suka je Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022, da kuma Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai ta 2024.