fidelitybank

Ciwon hanta na kashe mutane fiye 35,000 a kullum harda Najeriya – WHO

Date:

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta ce mutane fiye da 3500 ne ke mutuwa a kowacce rana saboda cutar hanta, a fadin duniya, al’amarin da WHO ta ce abin tsoro ne domin adadin na karuwa.

Hukumar lafiya ta duniyar ta yi kiran da a dauki matakin da ya dace domin yaki da cutar wadda ke shafar hanta.

Ana ganin cutar da aka fi sani Hepatitis a matsayin ta biyu a cikin jerin cutuka mafi muni da saurin kisa a duniya.

Wakiliyar BBC ta ce fiye da mutum miliyan dari uku da hamsin ne a duniya ke fama da nau’in cutar hanta nau’in B ko C, wadda ke janyo kamuwa da mummunar cuta da kuma kansar hanta.

WHO ta ce kashi biyu bisa uku na masu dauke da cutar a kasashen Bangladesh da China da Ehiopia da India da Pakistan da Indonesia da Nigeria da kuma Rasha suke.

Akwai dai magunguna masu kyau da saukin kudi da ake amfani da su wajen maganin cutar, to amma har yanzu kashi uku cikin 100 masu dauke da cutar nau’in B ne kadai ke samu maganinta.

world news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp