Fadar Shugaban ƙasa ta fitar da wata sanarwa, inda ta nemi ‘yan ƙasa da su daina rige-rigen sayen man fetur, tana mai cewa sai ƙarshen watan Yuni za ta janye tallafin man.
An fitar da sanarwar ce da zimmar kawo ƙarshen zullumin da jama’a suka shiga sakamakon jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya yi bayan rantsar da shi a ranar Litinin, inda ya ce “tallafin mai ya ƙare” ba tare da bayar da takamaiman lokacin ƙarewar tasa ba.
Jim kaɗan bayan jawabin nasa ne aka fara samun dogayen layukan motoci a gidajen sayar da man fetur a manyan biranen ƙasa.
Sai dai sanarwar ta ce, jawabin na shugaban ƙasaba sabon abu ba ne kuma ba gwamnatinsa ce ta ɗauki matakin ba.
Kazalika ta nuna cewa an tanadi kuɗin biyan tallafin ne zuwa watan Yunin 2023 kawai.
“Kawai ya na bayyana halin da ake ciki ne, ganin cewa kasafin kuɗin gwamnatin da ta gabata game da tallafin, an tsara shi ne zuwa wata shidan farko na wannan shekarar,” a cewar ofishin shugaban ƙasa.


