Kungiyar Al-Nasr da Ronaldo yake buga wasa ta shaida wa Hukumar Kwallon Kafa ta Iran cewa ba za ta yi atisaye na ƙarshe ba a filin wasa na Azadi gabanin wasansu da Persepolis.
Kamfanin dillancin labarai na Iran ISNA ya ce dalilin wannan mataki shi ne tarbar da aka yi wa Ronaldo da sauran abokan wasansa, kuma Ƙungiyar ba ta son shiga haɗarin fita daga otel zuwa filin wasa na Azadi ba.
A gefe guda kuma, Kocin Espinas da ke zaune a otel ɗaya da Al-Nasr ya ce an fasa wani ɓangare na otel ɗin saboda yawan magoya bayan Ronaldo.
Ali Asghar Amiri ya ce, “Cunkoson magoya bayan ya janyo an lalata wani ɗan karamin lambu da ke otel ɗin da kofofi da wani ɓangare na shiga ciki.”
A gobe ne Persepolis za ta karɓi baƙuncinAl-Nasr ta Saudiyya a wasan farko na rukuni na kofin zakarun Asia a filin wasa na Azadi, ba tare da ‘yan kallo ba


