Shugaba Bola Tinubu ya ce ba ya cikin kamus dinsa na cin zarafin gwamnatocin da suka shude biyo bayan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Tinubu ya ce ya gwammace ya dauki mataki ya sake farfado da kasar nan kan turbar nasara.
Da yake jawabi a Minna, jihar Neja, shugaban ya ce jajircewa da daidaito zai sa Najeriya ta zama kasa mai girma.
A cewar Tinubu: “Lokacin da ka karanta takardun, wasunmu sun ruɗe ko za su zagi halin yanzu ko na baya (gwamnati) ko kuma su ba da uzuri na gaba.
“Ba ya cikin ƙamus na, abin da na fi mayar da hankali a kai shi ne in ɗauki mataki a yanzu, ku yi iya ƙoƙarinku, ku sake inganta harkokin kuɗin ƙasar kuma ku tsaya a kan hanya madaidaiciya.
“Wadanda za su iya yin korafi a yanzu dole ne su fahimci cewa juriya da daidaito zai sa al’umma ta kasance mai girma.”