Hukumar kare hakkin dan adam a jihar Kano, ta ce, a shekarar da ta gabata sun karbi korafe-korafen tauye hakkin dan adam har dubu daya da dari biyar daga sassan jihar.
Shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa, akasarin korafe-korafe sun shafi cin zarafin kananan yara da kuma fyade, sai batun zamantakewar aure inda suka samu nasarar shawo kan matsaloli fiye da dubu daya.
Hukumar kare hakkin dan adam din reshen jihar Kano ta ce daga watan Janairu zuwa watan Disambar bara sun karbi korafe-korafen take hakkin bani-adama har dubu daya da dari biyar, wadanda suka shafi zamantakewa ta iyali.
Sai dai kuma hukumar ta ce akwai wasu matsalolin da suka shafi cin zarafin mata da kananan yara, kamar yada Shehu Abdullahi babban jami’in a hukumar ya shaidawa BBC.
Shehu Abdullahi ya ce cikin korafe-korafen dubu daya da dari biyar, sun yi aiki walau na shari’a ko na zama tare da tattaunawa da wadanda abin ya shafa har dubu daya da dari biyu da casa’in da shida.
Kana matsaloli fiye da dari biyu ana ci gaba da aiki akansu.
Jami’in ya kuma ce akwai bukatar samar da kyakkyawan yanayi na aikin yi da walwalar tattalin arziki tsakanin al’umma, musamman mata ta hanyar samar musu da ayyukan yi a gidanjensu.
Bayanai na cewa a baya, ‘yan uwa da dangi da kuma abokan arziki kan warware tare da sasanta duk wani korafi ko rikici, amma a yanzu hakan ya yi karanci, al’amarin da yasa ake tururuwar kai korafe-korafe zuwa hukumar kare hakkin dan adam.