Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon Yusuf Abdullahi Ata, ya yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta soke zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin jihar Kano da aka gudanar a mazabar Bagwai/Shanono, inda ya bayyana shi a matsayin cuwa-cuwar siyasa.
Ata, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Kano a ranar Lahadi, ya ce jam’iyyun siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaɓen, amma jam’iyyar NNPP ta karya yarjejeniyar ta hanyar shigo da matasa dauke da makamai daga makwabtan Jihohi. Ya ce hakan ya kai ga kai hari ga magoya baya da kuma gidan ɗan takarar APC.
Ya bayyana cewa a ranar zaɓe an shigo da dubban ’yan daba dauke da makamai tun da asubahi, lamarin da ya tilasta jama’a gudu daga kauyuka. A cewarsa, ’yan daba sun kwace kayan zaɓe da suka haɗa da takardun zaɓe da sakamakon sannan suka cika su da dangwalawa ƙuri’un jam’iyyar NNPP.
Ministan ya ce al’ummar mazabar da suka shafe sama da shekara guda suna jiran gudanar da zaɓen sun kasance cikin takaici da rashin adalci. Ya roƙi magoya baya da su kwantar da hankulansu tare da kira ga hukumomin tsaro da su gurfanar da duk wasu da aka kama.