An tsige mataimakiyar shugabar Majalisar Tarayyar Turai, bayan an zarginta da karbar cin hanci da halatta kudin haram, a wata kuri’a da aka kada a majalisar ta turai.
Eva Kayiili, yar majalisa daga Girka ta musanta karbar cin hanci daga Qatar, domin yin tasiri da kuma kare martabar gwamnatin Doha.
‘Yan sandan Belgium sun gurfanar da ita da wasu mutane uku da ake zargi, bayan wani samame a Brussels inda aka gano makudan kudade.
Nan gaba a yau ne Majalisar Tarayyar Turai za ta gudanar da muhawarar gaggawa game da badakalar, inda za a yi nazari kan ra’ayoyi da kuma yadda za a kara sa ido tare da tabbatar da gaskiya game da kudaden Tarayyar.
Qatar dai ta musanta zargin bayar da cin hancin.