fidelitybank

Cin Amana: Matashi ya kashe abokin sa ya gudu da motarsa da Naira miliyan 2 zuwa Kano

Date:

Man in cuffs

Bashir ne babban abokin mamacin yayin da ya yi aure ‘yan watannin da suka gabata.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Bashir ya gayyaci mamacin ne mai shekara 28 da haihuwa zuwa unguwar Tudun Fulani ta birnin Minna kimanin mako biyu da ya gabata domin su tattauna kan wata damar kasuwanci da ta bayyana a cewarsa.

Sai dai Bashir ya daba wa amamacin wuka bayan da ya isa wurin, kuma ya tsere da motarsa kirar Peugeot 206 da kuma Naira miliyan biyu da ke cikin motar.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke jihar ta Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin ta hannun kakakinta DSP Wasiu Abiodu, wanda yace bincike ya sa sun kama Bashir da wani wanda ya taimaka masa mai suna Aliyu Ibrahim wanda ke da shekara 22 da haihuwa.

Akwai kuma wani Suleiman Mahmud da shi ma ake tuhuma da hannu wajen aikata wannan aika-aikar, wanda tuni ya tsere, sai dai ‘yan sanda na ci gaba da nemansa.

Jaridar ta kuma ce Bashir ya tsere da motar ne zuwa Kano, domin ya sayo wasu sinadarai da ake wanke zinare da su da kudin mamacin.

Sai dai bayan ya koma Minna ne ‘yan sanda suka damke shi a wani otel da ke kan babbar hanyar Wetern Bypass a Minna.

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp