Ƴan kasuwa a Najeriya sun shigar da madara ta kimanin naira biliyan 27, 664.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS na cewa an shigar da madarar ne daga ƙasashe huɗu.
An kashe waɗannan kuɗaɗen ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayyar ƙasar ke shirin haramta shigar da madara cikin ƙasar.
Gwamnatin Najeriyar ta so ta haramta shigar da madarar ne sakamakon kayayyakin samar da madarar da gwamnatin ta ce ta samar a kwanakin baya.