fidelitybank

Cikin wata 2 an kama mutane 562 a Akwa Ibom

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, ta kama mutane 562 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin kwata na karshe na shekarar 2023.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Olatoye Durosinmi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Asabar a Uyo.

A cewarsa, jami’an rundunar sun cafke wadanda ake zargi da laifuka daban-daban da suka hada da kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami, fyade da kuma sata.

Ya ce da dama daga cikin wadanda ake zargin an gurfanar da su a gaban kotu, kuma an bayar da belin wasu daga cikinsu, yayin da wasu kuma ke ci gaba da bincike.

Ya lissafa wasu laifukan da suka hada da fasa bututun mai da kuma zagon kasa ga tattalin arziki da wani Godwin Ita Effiong ya yi, wanda ya hada baki da wasu mutane hudu suka lalata bututun mai na Frontier Oil tare da sace jarkoki 18 na danyen mai lita 25 a ranar 18 ga watan Nuwamba.

CP ya kara da cewa, a lokacin da ake binciken, wani Francis Eze da Johnson Amadu da ake zargin suna dauke da bindiga a cikin gida, sun yi wa wani ma’aikacin POS fashi, Glory Akpan, sannan suka tafi da injin POS dinta, wayar Android da Naira 300,000.

nnn-news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp