Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar Labour Party, LP, Peter Obi, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 20,000 kasa da cikin shekaru hudu ba idan aka zabe shi a zabe mai zuwa.
Obi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin shirin gidan talabijin na Channels, âThe Peopleâs Townhall 2023.
Ya ce, “A cikin shekaru hudu, za mu iya samar da kuma rarraba kasa da 20,000MW”.
A cikin kwata na farko na shekarar 2022, kamfanonin samar da wutar lantarki guda ashirin da shida, GenCos, sun samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 4,712.34, kamar yadda rahoton hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta fitar na watanni uku.