Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce za a iya cim ma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine cikin ‘yan makonni masu zuwa.
Ya fadi haka ne a kafar talbijin ta Fox News bayan ya gana da Shugaban Amurka Donald Trump a Fadar White House.
“Mun yi aiki tukuri tare da Birtaniya, muna son gabatar da shirin Birtaniya da Faransa na aike dakaru ba wai domin su shiga sahun gaba a yakin ba, sai don tabbatar da zaman lafiya a iyakokin kasashen biyu,” in ji Mista Macron.
Ya nanata cewa shugabannin Turai a shirye suke su shiga batun tabbatar da tsaron Ukraine.