fidelitybank

Cikin ƙasa da sa’o’i 13 Sojojin Najeriya za su iya ƙwace Nijar – Bashir El-Rufa’i

Date:

Bashir, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi ikirarin cewa sojojin Najeriya na iya kwace babban birnin Jamhuriyar Nijar, Yamai cikin sa’o’i 13.

El-Rufai ya nakalto wani faifan bidiyo da wani ma’abocin Twitter ya watsa yana yabon sojojin Jamhuriyar Nijar, El-Rufai ya ce, baya addu’ar yaki amma yana fatan sojojin Najeriya za su baje kolinsu tare da kwace Nijar cikin kasa da sa’o’i 13.

“Duba sojojin Tinubu suna son su je su yi fada da sojojin Najeriya,” in ji mai amfani da Twitter @chimaobi_nteoma.

El-Rufai ya mayar da martani: “Allah ya kiyaye yaki amma saboda faifan bidiyo irin na wauta ne nake fatan sojojin Najeriya za su baje kolinsu a Nijar su kama Yamai cikin sa’o’i 13.”

Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta yanke hulda da Najeriya bayan kokarin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta yi na maido da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ya ci tura.

Sakamakon haka, shugaban Najeriyar kuma shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, Bola Tinubu ya rubuta wa majalisar dattawan bukatar goyon bayanta ga tsoma bakin soja a kan mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp