Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya yi gargadin cewa ci gaba da dogaro da man fetur kadai zai kara talauci, da rashin aikin yi a Najeriya.
Abbas ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron karramawar digiri karo na 14 na Jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin, ranar Litinin.
Ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta fara amfani da dimbin albarkatun da take da su tare da karfin dan Adam domin fadada tattalin arzikinta.
Ya kara da cewa, don tabbatar da makomar tattalin arzikin kasar, dole Najeriya ta daina dogaro da mai kawai ta kuma bullo da sabbin hanyoyin bunkasa ci gaba mai dorewa.
Ya ce, “Tare da raguwar kudaden shiga daga man fetur, sauyin yanayin duniya zuwa makamashi mai sabuntawa, da kuma bukatar samar da ayyukan yi, dole mu yi gaggawar tsara sabon tsari don sauya tattalin arzikinmu.
“Wannan yana bukatar kokari na musamman don bude damammakin wasu bangarori, kamar noma, ma’adanai, fasaha da masana’antar kere-kere.
“Samun wannan sauyin zai tabbatar da makomar tattalin arzikin Najeriya, tare da magance matsalolin talauci, da rashin aikin yi, wanda su ne manyan kalubale ga ci gaba mai dorewa,” in ji shi.