Magatakardar hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce hukumar ta baiwa cibiyoyin jarabawar na’ura mai kwakwalwa (CBT) damar kara kudin rijista zuwa 1,000 a ranar 9 ga Afrilu.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa, NAN, ya ruwaito cewa, JAMB na shirya jarabawar wanda zabin ne don gwada kayan aiki a cibiyoyin da aka amince da su da za a yi amfani da su a jarabawar a fadin kasar.
Hukumar ta shirya fara babban jarabawar UTME daga ranar 6 ga Mayu zuwa 16 ga Mayu.