Kulob din Seria A, Salernitana ya sanar da daukar dan wasan gaba Chukwubuikem Ikwuemesi.
Tsohon dan wasan Flying Eagles ya koma Garnets daga kulob din Slovenia NK Celje.
Dan wasan mai shekaru 22 ya sanya alkalami a takarda kan kwantiragin shekaru hudu.
An baiwa Ikwuemesi riga mai lamba 22 a kulob dinsa.
Ya zura kwallaye tara kuma ya taimaka wa NK Celje a kakar wasan da ta wuce.
Ikwuemesi zai kasance dan Najeriya na biyu da zai buga wa Salernitana wasa bayan William Troost-Ekong ya yi zaman aro a kungiyar a kakar wasan da ta wuce.