Majalisar dattawa ta amince da Bankin ci gaban ƙasar China a matsayin sabon mai bayar da kuɗi wajen gina layin dogo a ƙasa, wanda zai ci kusan dala biliyan ɗaya.
Wani mai ba da lamuni na ƙasar China ya kamata ya ɗauki nauyin layin tsakanin Kaduna da Kano – birni mafi girma a arewa – amma ya janye a shekarar 2020.
Lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki shekaru takwas da suka gabata, ya ba da fifiko wajen inganta hanyoyin sufuri da samar da wutar lantarki a ƙasa.
Duk da haka, samar da kuɗaɗe ya kasance babban cikas wajen gudanar da ayyukan.
Majalisar ta amince ta ciyo rancen biliyoyin dala daga China da sauran masu ba da rance na ƙasa da ƙasa amma har yanzu kuɗaɗen ba su samu ba.
A lokacin da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayu, zai gaji tarin kalubale da suka haɗa da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin tsaro da a ke fama da shi.