Ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta ce ta yi Allah-wadai da harin da aka kai kan asibitin Gaza ko da yake ba ta fito fili ta zargi Isra’ila, ko kuma ‘yan gwagwarmayar FalasÉ—inawa ba.
Kakakin ya ce, China ta yi kakkausar suka kan harin da aka kai a asibitin Gaza, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane masu yawa.
“Muna jimamin waɗanda suka mutu sakamakon harin, kuma muna jajantawa waɗanda suka jikkata.
China ta yi kira da a tsagaita buÉ—e wuta cikin gaggawa, da dakatar da tashin hankali, da duk wani Æ™oÆ™ari na kare fararen hula, da kaucewa wani bala’in jin Æ™ai mafi muni.”


