Ƙasar China ta zama ƙasa ta farko da ta naɗa jakada a ƙasar Afganistan, tun bayan da ƙungiyar Taliban ta karɓa mulki a shekarar 2021.
Taliban ta ce naɗin Zhao Xing wata alama ce ga sauran ƙasashe na ƙulla alaƙa da gwamnatinta.
Babu wata ƙasa da ta amince da gwamnatin Taliban da ake zargi da take hakkin bil’adama da dama a Afghanistan.
Kasar China na daga cikin ƙasashen da suka fara hulɗa da su bayan sun hau karagar mulki a shekarar 2021.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar China a ranar Larabar ta bayyana cewa, Beijing za ta ci gaba da yin shawarwari da hadin gwiwa” da Afganistan, kuma manufarta game da kasar a bayyane take.
Majalisar Dinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun yi Allah-wadai da ƙungiyar Taliban kan yadda take musgunawa mata.


