Ƙasar China ta soma atisayen soji na musamman a cikin teku kusa da Taiwan bayan ziyarar da shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai tsibirin.
Ms Pelosi ta bar Taiwan ɗin a ranar Laraba, bayan wata gajeruwar ziyara mai cike da taƙaddama da ta kai tsibirin, wadda China ke kallo a matsayin wani lardinta da ya ɓalle.
Domin mayar da martani, sai ƙasar China ta sanar da gudanar da atisayen soji na tilas wanda za a soma a yau Alhamis.
Tsibirin na Taiwan ya ce, jiragen yaƙin China ɗai-ɗai har 27 suka shiga ta sarararin samaniyarsa, sai dai tun a ranar Laraba ma’aikatar tsaron Taiwan ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro ta hanyar watsa jiragenta a sararin samaniya, domin gargaɗin na China da ke mata barazana. In ji BBC.


