Rundunar sojin kasar China ta ce, tana cigaba da gagarumin atisayen soji a kusa da Taiwan, biyo bayan sanarwa da ta yi na kawo karshen atisaye da harsasai a jiya Lahadi.
Dakarun Sojin gabashin gasar sun bayyana cewa za su yi atisayen kai hari akan jiragen ƙarƙashin ruwa da hare-haren teku. In ji BBC.
Atisayen da aka gudanar a kwanaki hudu da suka gabata martani ne ga ziyarar da Kakakin Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai tsuburin.
Taiwan na zargin China da amfani da wannan atisayen domin shirin kutsawa cikin tsuburin.