Dan wasan tsakiya na Chelsea, Mason Mount, na iya shirin ficewa daga kulob din a wannan bazarar yayin da mai kula da kulob din, Todd Boehly ya bayar da rahoton cewa yana shirin fsiyar da wasu ‘yan wasa 14.
Chelsea ta fanshe sama da fam miliyan 500, tun lokacin da Boehly ya karbi ragamar aiki daga hamshakin attajirin Rasha Roman Abramovich a bazara.
Hakan ya hada da rikodi na fam miliyan 323 da aka kashe a kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu kadai kan sabbin ‘yan wasa takwas.
A cewar Telegraph, Chelsea za ta yi kokarin sallamar ‘yan wasa da dama wadanda suka hada da Mount, Thiago Silva, Mateo Kovacic, Cesar Azpilicueta, Ruben Loftus-Cheek, Pierre Emerick-Aubameyang da Christian Pulisic, da zarar an bude taga bazara.
Sauran ‘yan wasan sun hada da N’Golo Kante da Kai Havertz da Ben Chilwell da Conor Gallagher da Edouard Mendy da Hakim Ziyech da Kepa Arrizabalaga domin yarjejeniyarsu za ta kare ne a watan Yunin 2025, duk da cewa ba dukkaninsu za su tafi tare ba.
Rahoton ya kara da cewa Chelsea ta kuduri aniyar kaucewa ‘yan wasa shiga watanni 12 na karshen kwantiraginsu ta kowacce hanya, da kuma wadanda suka rage shekaru biyu kacal a kwantiraginsu.