Mamalakin Chelsea, Todd Boehly na shirin sallamar ‘yan wasa kusan 10 a bazara.
Wannan yana nufin cewa zai zama wata babbar kasuwa ga Blues saboda masu kulob din suna son sake fasalin kungiyar.
Baya ga bude kofofin ficewa ga ’yan wasan farko da ba a so, masu kulob din Blues na shirin sake fantsama tsabar kudi kan sabbin ‘yan wasa.
Evening Standard ta ruwaito cewa suna tunanin siyar da ‘yan wasa 10 a lokacin bazara sakamakon mummunan kakar wasa.
Wadannan ‘yan wasan sun hada da Conor Gallagher, Ruben Loftus-Cheek, Edouard Mendy, Hakim Ziyech, Pierre-Emerick Aubameyang, Christian Pulisic da kuma Kalidou Koulibaly.
Boehly da takwarorinsa za su kuma yanke shawarar abin da zai kasance nan gaba ga N’Golo Kante, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara.
Rahotanni a Jamus sun nuna cewa ana kuma tunanin makomar Kai Havertz sakamakon rashin daidaituwar sa a kakar wasa ta bana yayin da Mason Mount shima zai iya barin Stamford Bridge.


