Chelsea ta tabbatar da cewa Paul Winstanley ya koma kungiyar a matsayin Daraktan fannin siya da siyar da ‘yan wasa na kungiyar.
Chelsea ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta shafinta na internet a ranar Talata.
Winstanley ya koma Chelsea ne bayan ya shafe shekaru takwas ya na kungiyar Brighton a gasar Premier.
Sanarwar ta kara da cewa: “Chelsea ta yi farin cikin sanar da cewa an nada Paul Winstanley a matsayin Daraktan Hazaka da siya da siyar da ‘yan wasa.
Chelsea FC na son gode wa Brighton saboda ba shi damar yin amfani da wannan sabuwar dama tare da Chelsea.
Da ya ke mayar da martani game da sabon nadin nasa, Winstanley ya gaya wa Chelsea cewa, ya yi farin cikin shiga kungiyar ta yammacin London.
Ya ce: “Ina fatan yin aiki tare da irin wannan fitattun gungun abokan aiki yayin da kungiyar .”
Winstanley ya yi aiki tare da kocin Chelsea Graham Potter a lokacin da suke tare a Brighton.