Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Chelsea ta kammala ɗaukar ɗan wasan gaba na Ivory Coast David Datro Fofana daga ƙungiyar Molde da ke Norway a kan kuɗin fam miliyan takwas zuwa 10.
Ɗan wasan mai shekara 20 – wanda kuma ya ci kwallo 24 a wasa 65 da ya buga wa Molde – ya saka hannu kan kwantiragin shekara shida da ƙungiyar ta stamford bridge zuwa shekarar 2029, tare da zaɓin tsawaita kwantiragin.
Shi ne ɗan wasa na biyu da ƙungiyar ta saya cikin wannan wata na Janairu bayan ɗan wasan bayan Faransa Benoit Badiashile da ta saya daga Monaco kan fam miliyan 35.
“Ina cike da farin cikin zuwa ƙungiyar da na daɗe ina mafarkinta” in ji Fofana.
Chelsea ta bayyana ɗan wasan da cewa ”mai hazaƙar zura in ƙwallaye, kuma ɗaya daga cikin matasan ‘yan ƙwallon da suke da makoma mai kyau a nan gaba”.
Haka kuma ƙungiyar na kan tattaunawa da da Benfica kan ɗaukar matashin ɗan wasan tsakiyar Argentina Enzo Fernandez mai shekara 21, wanda ƙa’idar da ke cikin yarjejeniyar cinikinsa ta kai fam miliyan 106.