A ranar Alhamis ne Chelsea ta sanar da daukar Deivid Washington daga kungiyar Santos ta Brazil kan kwantiragin shekaru bakwai, tare da zabin karin shekara.
Chelsea ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na yanar gizo gabanin wasansu na gasar Premier da Luton Town ranar Juma’a.
Washington, mai shekaru 18, na iya taka leda a ko’ina a kan layi a mataki na uku na karshe, amma galibi a matsayin dan wasan gaba.
Ya fara aikinsa da Gremio kafin ya koma Santos a 2016.
“Barka da zuwa Chelsea, Deivid,” sanarwar Chelsea ta karanta a wani bangare.


