Ɗan wasan Chelsea, Billy Gilmour, ya shaida wa shugabannin kulob din, ciki har da mai kula da kungiyar Todd Boehly, cewa yana son barin Blues, in ji The Evening Standard.
Gilmour yana son barin Chelsea a wannan bazarar don neman buga kwallon kafa a koda yaushe.
Evening Standard ta ruwaito cewa Brighton ta tabbatar da sha’awarta na siyan dan wasan tsakiyar mai shekaru 21 a kan yarjejeniyar dindindin.
Gilmour ya kasance tare da Chelsea tun lokacin da ya sanya hannu daga Rangers a 2017 kuma ya buga manyan wasanni 22 a kulob din Stamford Bridge.
A halin yanzu Gilmour yana da sauran shekaru biyu kan kwantiraginsa da Chelsea.
Ba a ba dan wasan na Scotland lambar rigar ba a kakar wasa mai zuwa bayan da aka yi watsi da shi daga tawagar farko ta Thomas Tuchel.
Ku tuna cewa Callum Hudson-Odoi ya shaida wa Boehly cewa yana son barin kungiyar.


