Chelsea na zawarcin dan wasan Arsenal Emile Smith Rowe.
Blues na son kammala cinikin dan wasan gabanin ranar Juma’a.
Tuni dai Chelsea ta kashe kusan fam biliyan 1 tun lokacin da Todd Boehly ya koma kungiyar.
A wannan bazarar kadai, ƙungiyar da ke yammacin London ta kashe fam miliyan 350.
Mauricio Pochettino na son kara wani zabin kai hari sakamakon raunin da Christopher Nkunku ya yi na tsawon lokaci.
A cewar Daily Mail, Blues, baya ga tunanin neman Smith Rowe, suna kuma tunanin kawo ‘yan wasan Barcelona biyu Raphinha da Ferran Torres.
Kwana biyar kacal ya rage a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa ta bazara.


